Afrika

Mutane miliyan 355 suka ci gajiyar Bankin raya Afrika -Adeshina

Bankin Raya kasashen Afrika yace ya taimaka wajen inganta rayuwar mazauna nahiyar sama da miliyan 355 wajen gudanar da ayyukan sa da kuma taimakawa kasashe dan ganin sun aiwatar da ayyukan cigaba.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina. AFP/Issouf Sanogo
Talla

Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ya ce ana bukatar irin manyan ayyukan da gwamnatoci ke aiwatar wa da su taimaka wajen inganta rayuwar jama’ar dake kasashen su musamman samar musu da cigaba da kuma rayuwa mai inganci.

Adeshina ya ce bukatar ganin an inganta rayuwar jama’ar dake Afrika ya sa lokacin da aka zabe shi ya kaddamar da shirye shirye da dama da suka hada da samarwa kasashen nahiyar wutar lantarki da shirin samar da abinci wajen inganta harkar noma da samarwa Afirka masana’antu domin sarrafa kayan da ake nomawa da bunkasa kasuwanci a tsakanin jama’ar nahiyar.

Shugaban bankin yace wadannan matakai sun taimaka masa gaya wajen samun nasara a shekaru 5 da yayi yana jagorancin bankin kafin samun wa’adi na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI