Ghana-Najeriya

Obasanjo ya gargadi Akufo-Addo da Mahama kan rikicin zabe a Ghana

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Getty Images

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gargadi shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da abokin karawar sa kuma tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama da su kaucewa tashin hankali a zaben shugaban kasar da za’ayi ranar 7 ga watan gobe.

Talla

A wata budadiyar wasikar da ya rabawa manema labarai, Obasanjo ya bukaci shugabannin biyu da su janyo hankalin magoya bayan su wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

A shekarar 2016, Akufo-Addo na Jam’iyyar NPP ya kada shugaba mai ci John Mahama na NDC, kuma shugabannin biyu zasu sake fafatawa a tsakanin su a zaben watan gobe.

Obasanjo ya yiwa Ghana fatar alheri a zaben mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.