Najeriya

Sake Farfado da sashen noma a Najeriya

Noman shinkafa a wasu kasashen Afrika irin su Burkina Faso
Noman shinkafa a wasu kasashen Afrika irin su Burkina Faso dr

A Najeriya,wasu gwamnonin jihohin kasar sun kaddamar da wani tsari da zai taimaka don wadatar da jama’a da isashen cimaka a wannan lokaci da ake sa ran Najeriya zata bude kan iyakokin ta.

Talla

Shirin dake zuwa a dai-dai lokacin da Majalisar dinkin Duniya ta ware rana dangane da cimaka a Duniya.

A jihar Anambra dake Najeriya kusan manoma dubu shida ne za su amfana da tallafi daga hukumomin wannan yankin .

Wannan tasrin zai taimaka a cewar Willie Obiano gwamnan jihar don kawo karshen karancin cimaka tareda baiwa manoma damar amfana da kayyakin ayukan noma na zamani da kuma bunkasa noman shinkafa a dai dai lokacin da ake ta nanata cewa Najeriya na shirin bude kan iyakokin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.