Habasha - Tigray

Sojojin Habasha sun kaddamar da gagarumin farmakin yankin Tigray

Franministan Habasha Abiy Ahmed
Franministan Habasha Abiy Ahmed AFP/Monirul BHUIYAN

Gwamnatin Yankin Tigray dake Habasha tare da kungiyoyin agaji sun ce dakarun gwamnati sun kaddamar da munanan hare haren sama kan tsakiyar birnin Mekele dake dauke da mutane akalla dubu 500.

Talla

Sanarwar gwamnatin yankin tace sojojin Habasha yau Asabar sun kaddamar da munanan hare haren sama da makaman atilare a yunkurin su na murkushe shugabannin yankin da suka ki aje makaman su.

Gwamnatin yankin ta bukaci kasashen duniya da suyi Allah wadai da wannan mataki da Firaminista Abiy Ahmad ya dauka na amfani da makaman atilare da jiragen yaki kan fararen hula domin kisan kare dangi.

Kungiyar agaji ta ICG tace dubban mutane suka mutu tun bayan kaddamar da yaki tsakanin bangarorin biyu makwanni 3 da suka gabata, yayin da kasashen duniya ke kiran kai zuciya nesa da kuma tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka dubban Yan kasar Habasha sun tsallaka Sudan a matsayin yan gudun hijira domin kaucewa tashin hankalin, yayin da mayakan Tigray ke harba rokoki zuwa cikin Eritrea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.