Najeriya

An yi garkuwa da mutane 1570 a Najeriya a cikin shekara ta 2020-rahoto

Kungiyoyin dake dauke da makamai a arewacin Najeriya
Kungiyoyin dake dauke da makamai a arewacin Najeriya REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Wani bincike ya nuna cewar akalla Yan Najeriya 1,570 masu garkuwa da mutane suka sace a cikin watanni 11 da suka gabata, wato daga watan Janairun wannan shekara zuwa watan Nuwamba mai karewa.

Talla

Binciken da jaridar Daily Trust ta wallafa yace masu garkuwa da mutanen sun yi nasarar samun kudin da ya kai sama da naira miliyan 311 a matsayin kudin fan sa daga ‘yan uwa da iyalan mutanen da suka yi garkuwa da su, duk da yake kudaden da suka bukata a biya su a matsayin diyya ya kai kusan naira biliyan 7.

Wadannan kudade inji rahotan bai kunshi wadanda wasu daga cikin mutane suka biya ba, amma suka ki cewa komai kan diyyar da suka gabatarwa barayin saboda barazanar da suka musu ko kuma domin kaucewa fushin ‘yan bindigar.

Jaridar tace an samu karuwar matsalar garkuwa da mutane a Najeriya da kashi 41 a watan Nuwamba kawai, abinda ya sa matsalar ta zama ruwan dare gama duniya, kuma ta kaiga shiga manyan makarantu a Kaduna da kuma babban birnin tarayyar Abuja inda aka samu rahotan garkuwa da mutane 31 a wannan shekara.

Rahotan yace yanzu haka matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare akan hanyar Abuja zuwa kaduna da Abuja zuwa Lokoja abinda ke jefa rayuwar jama’ar dake yankin da kuma matafiya cikin hadari kowacce rana.

Jaridar tace daga yarinya ‘yar shekaru 7 da aka sace aka kuma bukaci naira miliyan 3 a matsayin diyya a Jihar Katsina zuwa wata gyatuma Zainab Musa mai shekaru 60 a Jihar Niger, yan Najeriya musamman mazauna Yankin arewacin kasar na zama cikin fargaba dare da rana.

Rahotan yace su kan su jami’an tsaro basu tsira ba, ganin yadda aka sace manyan jami’an Yan Sanda 12 da Jami’an kare hadura 10 da jami’an tsaron fararen kaya 4 tare da na DSS.

Wannan ya sa Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da kungiyar Yan arewacin kasar ta ACF suka sake bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro a wannan mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.