Afrika

Abiy Ahmed ya bayyana nasarar dakarun Habasha kan yankin Tigre

Firaministan Habasha  Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed Ebrahim Hamid / AFP

Firaministan ya bayyana kawo karshen farmakin da dakarun Habasha suka kai Makele dake yankin Tigre.Abiy yace sun samu nasarar murkushe shugabanin yankin dake dauke da makamai cikin dan karamin lokaci.

Talla

Majiya daga yankin na nuni cewa dakarun Habasha sun kama wasu manyan wurare a yankin na Tigre,kazalika gidan talabijen na Tigre Tv ya dakatar da watsa shirye-shiryen sat un bayan da dakarun Habasha suka shiga garin.

Firaministan kasar da Babban hafsan sojin kasar ta Habasha sun tabbatar da cewa farmakin bai shafi farraren fula ba, sai dai Shugabanin yankin Tigre da suka gudu sun sanar da cewa za su mayar da martani tareda a abinda suka kira kisan farraren hula tareda lalata kadarori da sojojin Habasha suka aikata a wannan farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.