Turai

Faransa da Birtaniya sun cimma yarjejeniar hana shigar baki daga La Manche

Faransa da Birtaniya sun cimma yarjejenia da nufin kawo karshen kwarrar yan cin rani dake amfani da gabar ruwan La Manche don shiga kasashen biyu.Yarjejeniyar ta kunshi samar da runduna ta musaman tsakanin kasashen biyu don kulawa da gabar ruwan La Manche,wanda zai kai kasashen biyu ga lunka adadin jami’an da ake da su a baya kama daga farkon watan Disembar shekarar bana.

Wasu daga cikin hanyoyin da yan cin rani ke amfani da su don shiga yankin Turai
Wasu daga cikin hanyoyin da yan cin rani ke amfani da su don shiga yankin Turai REUTERS
Talla

Da jimawa Birtaniya ta zargi Faransa da sakaci,ganin ta yada ake fuskantar kwarrarar yan ci rani dake amfani da gabar ruwan La Manche don shiga Faransa ko Birtaniya.A watan Satumba ,Faransa ta bayyana cewa ta kama yan cin rani 1.300 da suka yi kokarin tsallakawa Birtaniya daga gabar ruwan la Manche,a wannan yanki dake arewacin Faransa,duban yan cin rani ne ko kokarin ganin sun samu kan su a Birtaniya,inda suke amfani da kwalo-kwalo ko hada baki da direbobin manyan motocin sufuri dake tsallakawa daga Faransa zuwa Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI