Afrika

Mutane 22 ne suka mutu a wani fada tsakanin manoma da makiyayan Chadi

Wasu daga cikin makiyayan kasar Chadi
Wasu daga cikin makiyayan kasar Chadi RFI/Charlotte Cosset

Akala mutane 22 ne suka mutu a wani fada da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kudancin Chadi a cewar ofishin Ministan sadarwa na kasar.Da samun labarin,gwamnatin Chadi ta aike da jami’an tsaro zuwa jihar Kabbia tareda aiwatar da dokar ta baci.

Talla

Ana zargin manoman yankin da hadasa fada bayan da suka yi garkuwa da wasu shanun makiyayan da suka lalata kayan gona.

A kokarin kantoman yankin na shawo kan bangarorin biyu,manoman sun afkawa makiyayan bayan haka.

Fadan tsakanin makiyaya da manoman ya yi sanadiyar raunata mutane 34,yayinda hukumar yan sanda ta sanar da kama mutane 66.

Kasar ta Chadi na daga cikin kasashen Afrika musaman yankin Sahara da aka fi samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a duk shekara,wanda ke kuma hadasa asarar rayuka da dinbin dukiyoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.