Afrika

Yan Sandan Togo sun kama yan adawa a Lome

Yan adawa a kasar Togo
Yan adawa a kasar Togo REUTERS/Luc Gnago

Jami’an tsaron Togo sun kama daya daga shugabanin yan adawa Brigitte Adjamagbo-Johnson ,rahotanni sun ce an kama ta ne da marecen jiya asabar a tsakiyar birin Lome na kasar.

Talla

Jami’an tsaro sun bayyana cewa da jimawa suka kaddamar da binciken sirri bayan samun labaren dake cewa wasu daga cikin yan adawa na shirya manakinsa da nufin kawar da gwamnati mai ci.

Bincike ya gano cewa uwargida Brigitte Adjamagbo na dauke da tilin takardu da wasu bayyanai da za su taimaka a wannan kazamin aiki da yan adawa ke shiri aikatawa kamar dai yada majiyar tsaron kasar Togo ta tabbatar.

Yan adawa sun shirya zanga-zanga a jiya asabar ba tareda sun samu nasara a kai.

Kungiyoyin kare hakkokin bil Adam a kasar dama waje na ci gaba da kira ga hukumomin don ganin sun sako mutanen da ake tsare da su yanzu haka.

Yan adawa sun kalubalanci sakamakon zaben da ya gudana a watan Fabrairun shekarar bana ,zaben da hukumar zabe ta ayana Shugaba Faure a matsayin dan takara da ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.