Libya

Bangarorin da ke rikici da juna a Libya sun fara tattaunawar sulhu a Morocco

Dakarun Sojin Libya.
Dakarun Sojin Libya. Abdullah DOMA / AFP

Kungiyoyin da basa shiri da juna a kasar Libya sun fara wata sabuwar ganawa a kasar Morocco da zummar kawo karshen rikicin da ya tagayyara kasar su.

Talla

Taron na kwanaki biyu na gudana ne a birnin Tangier, kuma ya samu halartar wakilai 13 daga kowanne bangaren da ya shafi majalisar dokoki da bangaren zartarwa.

Kasar Libya ta fada cikin yakin basasa tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011, abinda ya bai wa kungiyoyin sa kai daukar makamai suna kai hare-hare.

A makon jiya, tawagar bangarorin biyu mai dauke da 'yan Majalisu 120 sun sha alwashin kawo karshen rikicin kasar da shirin gudanar da zabe bayan da taron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya ranar 24 ga watan nan a matsayin lokacin zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.