Burkina Faso

Kabore ya gaza samun rinjaye a majalisar dokokin kasar

Shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré.
Shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré. RFI

Shugaban Burkina Faso ya gasa samun rinjaye a majalisar dokokin kasar duk da cewa ya yi nasara a zaben shugabancin kasar da akayi a farkon wannan makon.

Talla

Sanarwar da hukumar zaben kasar ta fitar na nuna cewa jami’iyyar shugaba Marc Roch Kabore ta lashe zaben tun a zagayen farko, ta samau kujeru 56 cikin 127 na ‘yan majalisu, kasa da 64 dake bada rinjaye.

Hakan na nufin cewa dole, shugaba Kabore ya nemi goyan bayan jam’iyyun da sukayi kawance da shi domin samun Karin ‘yan majalisu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.