Habasha - Tigray

Mutane na ta kwarara asibitoci a yankin Tigray bayan farmakin sojin Habasha

Rahotanni daga Yankin Tigray dake kasar Habasha sun ce mutane na kwarara zuwa asibiti bayan da Firaminista Abiy Ahmad ya sanar da samun nasara kan mayakan yankin bayan kwashe makwanni 3 ana fafatawa a tsakanin su.

Sojojin kasar Habasha lokacin da suke dawowa daga yakin da suka kaddamar a yankin Tigray
Sojojin kasar Habasha lokacin da suke dawowa daga yakin da suka kaddamar a yankin Tigray Tiksa Negeri/Reuters
Talla

Kungiyar agaji ta Red Cross tace ma’aikatan lafiya a asibitin Mekele na fama da karancin abinci da magunguna da kuma jakankuna sanya gawarwaki.

Kungiyar tace tururuwan da marasa lafiya keyi ta tilastawa asibitin dakatar da wasu aikace aikace domin mayar da hankali akan wadanda suka samu raunuka.

Abiy Ahmed, wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar da ta gabata, ya bayyana samun nasara a yammacin Asabar, a gwabzawa da dakarunsa sukayi da mayaka karkashin jam’iyyar dake mulkin yankin Tigray na TPLF.

Kungiyoyin kasa-da-kasa suka ce, katsewar hanyoyin sadarwa a yankin ya hana damar tattara bayanai don tabbatar ikirarin gwamnati na cewa ta kwace iko da birnin na Mekele, bayan da aka harba roka zuwa makwabciyar kasar Eriteria yau Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI