Mali

'Yan ta'adda sun farmaki sansanonin Sojin Mali da makaman roka

Wasu Soji da ke yaki da ayyukan ta'addanci.
Wasu Soji da ke yaki da ayyukan ta'addanci. Reuters

Mayakan ‘yan ta’adda a Mali sun kai jerin hare-hare da makaman roka kan sansanonin sojin kasar da na kasashen waje da ke wasu manyen biranen yankin arewacin kasar, ciki har da birnin Gao.

Talla

Sauran biranen da masu tayar da kayar bayan suka kai wa farmakin makaman rokar kan sansanonin sojin na Mali da na hadin gwiwar kasashen Turai sun hada da Menaka da Kidal baya ga Gao abinda ba a saba gani a kasar ba.

Kawo yanzu rahotanni sun ce babu wanda ya rasa ransa a hare-haren, sai dai hasarar dukiyar da aka tafka.

A Kidal wani shaidar gani da ido ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar, gungun mahara haye kan babura ne suka soma yiwa sansanonin sojin Mali da na kasashen ketare barazana, daga bisani kuma farmaki da makaman roka ya biyo baya.

Mali ta jima tana fama da matsalar ta’addancin da ta soma daga arewacin kasar tun shekarar 2012, daga bisani matsalar ta bazu zuwa yankin tsakiyar kasar, abinda ya sanya Faransa girke dakarunta akalla dubu 5 na rundunar Barkane a kasar, zalika kasashen Turai ma suka aike da nasu dakarun na rundunar Takuba, sai kuma dubban dakarun majalisar wadanda ke tallafawa sojojin na Mali, sai dai har yanzu akwai yankunan arewacin kasar da basa karkashin ikon gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.