Nigeria-Gambia

Dalilan da suka sa na jagoranci raba Jammeh da mulkin Gambia - Buhari

tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Banjul. 13/12/2016.
tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Banjul. 13/12/2016. REUTERS/Stringer

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bayyana dalilan da suka saka ya jagoranci kungiyar ECOWAS wajen raba shugaba Yahya Jammeh daga kujerar mulkin Gambia.

Talla

Yayin da yake karbar shugaba Adama Barrow a Abuja, Buhari yace matakan da ya dauka na ganin Jammeh ya bar karagar mulki wani yunkuri na ganin kasar bata fada cikin tashin hankali ba wadda zata shafi Yankin baki daya.

Buhari yace sau biyu yake jagorancin tawagar ECOWAS zuwa Gambia domin ganawa da tsohon shugaban bayan ya fadi zabe domin bukatar ganin ya mika mulki ba tare da jefa kasar cikin rudani ba.

Shugaban Najeriya yace tun da sun rugumi siyasa mai Jam’iyyu da dama, ya zama wajibi su mutunta tanade tanaden da ke tafiye da su ba tare da nuna banbanci ba.

Buhari yace Najeriya zata cigaba da taimakawa Gambia duk da matsalolin cikin gidan da suka addabe ta, musamman ganin cewar kasar na shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa.

Shugaba Adama Barrow yace ya ziyarci Najeriya ne domin godewa kasar kan irin taimakon da ta basu ta hanyoyi da dama, musamman abinda ya shafi ilimi da bangaren shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.