Duniya

Adadin mutanen da suka mutu bayan kamuwa da cutar COVID-19 sun zarce milyan daya

Alurar yaki da covid 19
Alurar yaki da covid 19 JOEL SAGET / AFP

Adadin mutanen da cutar korona ta kashe a Duniya ya tasarwa miliyan daya da rabi, yayin da wadanda suka kamu da cutar suka zarta miliyan 64 a Duniya.

Talla

Hukumar lafiya ta duniya ta ce tun bayan barkewar cutar a China a watan Disamban bara, an samu mutane milyan 64 da dubu 522,200 da suka harbu da ita, daga cikin su kuma miliyan 1 da dubu 495,205 sun mutu.

Yayinda kamfanonin samar da alurar rigakafi da kamuwa da cutar ke ta kokarin ganin sun kamala ayukan karshe kafin a soma yiwa jama’a alura,yanzu haka wasu daga cikin kasashen Duniya sun bayyana shirin su na ganin jama’a sun wadata a kyauta da wadanan alurai,

Faransa ta ce za a yiwa mutan kasar alurar a kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.