Afrika

Cote D'Ivoire ta mayarwa Gbagbo da fasfo

Laurent Gbagbo tsohon Shugaban Cote D'Ivoire
Laurent Gbagbo tsohon Shugaban Cote D'Ivoire Jerry Lampen/Pool via REUTERS

A kasar Belgium,jakadan Cote D'Ivoire da wani jami'in ofishin ministan harakokin wajen kasar Cote D'Ivoire sun mayarwa tsohon Shugaban kasar Laurent Gbagbo da fasfon sa a wani Otel dake Belgium. 

Talla

Sake mayar masa da wadanan takardu na dada ba shi damar har indan ya na bukata komawa kasar sa ta Cote D'Ivoire. Kotun ICC dake shariar masu aikata laifukan yaki ta saki tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo, dan shekaru 73 dake tsare hannunta, bayan wanke shi da ta yi daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa na cin zarafin dan adam a rikicin zaben kasar na 2010-2011 da ya salwantar da rayukan jama’a sama da dubu 3.

A lokacin kotun ta gindaya wa Gbagbo sharudda kuma zai kasance a Belgium har sai bayan daukaka kara da ake jin masu gabatar da kara za su daukaka.

Cikin sharuddan aka giundaya masa akwai na bukatar ya kai kansa kotun idan an neme shi, kuma zai ajiye fasfon dinsa.

Laurent Gbagbo ya kasance na farko daga cikin tsohon shugabanin wata kasa da kotun ta garkame shi tun shekara ta 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.