Faransa

Jami’an tsaro zasu kaddamar da bincike kan Masallatai a Faransa

Wasu daga cikin musulmai a yayin ibada a wani masallaci
Wasu daga cikin musulmai a yayin ibada a wani masallaci REUTERS/Seun Sanni

Hukumomi a Faransa sun ce daga jiya alhamis jami’an tsaro zasu kaddamar da bincike kan Masallatai da wuraren ibadar da ake zargin cewar ana cusawa matasa tsatsauran ra’ayi sakamakon hare haren da aka kai a kasar ta Faransa .

Talla

Binciken da jami’an tsaron Faransa  zasu fara dai ya biyo bayan hare hare biyu da aka kai  a dan tsakanin nan,wadanda suka girgizar Faransa,kisan daya daga cikin malaman tarihi a wata makaranta musaman  file kan malamin da ya nuna hotan batanci ga Manzan Allah tsira da Amincin Allah suka tabbata a gare shi da kuma daba wukar da aka yiwa wasu mutane 3 a Mujami’ar Nice.

Wadanan hare-hare sun tilasatawa hukumomin kasar daukar matakan tsaro musaman tareda sa ido kan ayukan wasu daga cikin kungiyoyi a kasar ta Faransa.

A watan da ya gabata Shugaban kasar Emmanuel Macron ya gana da kungiyoyin limaman kasar,inda ya gabatar musu da tsarin da gwamnati ke da shi, shugaban ya kuma bukaci shugabanin sun nemi karin ilimi don fahimtar wasu daga cikin dokokin kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.