Wasanni

Kungiyoyi sun tsallaka mataki na gaba a gasar Europa

Wasa tsakanin Sevilla da Molde FK a gasar  Europa League
Wasa tsakanin Sevilla da Molde FK a gasar Europa League REUTERS / Marcelo del Pozo

A mataki na kusa da wasannin karshe, kungiyoyi da dama ne suka samu tsallakawa wasanin gaba a gasar cin kofin Europa.Ac Milan,Tottenham da Benfica yanzu haka sun samu tikiti buga wasannin gaba a wannan gasa.

Talla

Ac Milan ta samu nasara ne bayan da ta doke Celtic Glascow da ci 4 da 2,bayan da kungiyar Celtic ta ketse ragar Ac Milan bayan mituna 15 da ci 2 da nema.

Kungiyar ta Ac Milan ta samu wannan asara ne ba tareda dan wasar ta ba Ibrahimovic, dan wasan dake fama da rauni,sai dai dan wasa dan asalin kasar Noway Jens Petter Hauge ya taka gaggarumar rawa a wannan nasara ta Ac Milan.

Tottemham daga Ingila bayan wasar da ta yi da kungiyar Austria mai suna Lask aka kuma tashi 3 da 3,ta samu tsallakawa mataki na gaba a gasar ta Europa,kulob din zai yi kokarin neman gurbi na farko a rukunnin tareda sa ran samun nasara a fafatawar da Tottenham za ta yi da Anvers ranar Alhamis makon gobe.

Kazalika Benfica daga Portugal ta lalasa Lech Poznan daga Fologne da ci 4 da nema,nasarar dake baiwa kulob na kasar Fotugal damar tsallakawa mataki nag aba a wannan tafiya na Europa League,

Nasarar da Glascow Rangers daga Scotland ta samu a kan yan wasan Standard Liege na Belgium da ci 3 da 2 na baiwa yan wasan Scotland damar tsallakawa mataki nag aba.

A rukuni na uku ko rukuni C, kungiyoyin Leverkusen da Slavia Prague sun samu tikiti shiga zagaye na gaba bayan wadanan nasarori,

Leverkusen ta doke Nice daga Faransa da ci 3 da 2, yayinda Slavia Prague ta lalasa Hapoel Beer Sheva daga Isra’ila da ci 3 da nema.

A rukunni na 11 Dynamo Zagreb ta samu tsallakawa mataki na gaba bayan lalasa Feyenoord da ci 2 da nema.

Leicester duk da ta samu tikitin tsallakawa mataki na gaba ta yi kasa a gwiwa a fafatwar da ta yi Zorya Luhansk daga Ukrain da ci 1 da nema, yayinda Braga daga Fotugal ta doke AEK daga Athena da ci 4 da 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.