Faransa

Shugaba Macron ya sanar da zaman makokin kwana daya

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Christian Hartmann/Illustration

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana alhinin sa tareda sanar da zaman makoki na kwana daya bayan rasuwar tsohon shugaban Faransa Valery Giscard d’Estaing.Valery Giscard d’Estaing ya rasu ranar Laraba ya na mai shekaru 94, bayan kamuwa da coronavirus.

Talla

A yayin da yake jawabi zuwa Faransawa,Emmanuel Macron ya dangata tsohon Shugaban kasar da mutum dake da son kasar sa Faransa da yankin Turai.

Valery Giscard d’Estaing na daga Shugabanin Turai da suka taka muhimiyar rawa a duniyar diflomasiya da Afrika,a kasar sa Faransa da yankin Turai ya taimaka don samarwa mata inci da suka hada da samar da mukamai, incin zubar da ciki a hukumance.

Za a gudanar da jana’izarsa a sirce kamar yadda marigayin ya bar wa iyalansa wasiya.

Macron ya kara da cewa, mutuwarsa ta jefa Faransawa cikin zaman makoki, yayin da ya bayyana shi a matsayin hadimin al’umma kuma dan siyasa mai rajin tabbatar da ci gaba da samar da ‘yanci.

A ranar 30 ga watan Satumban bara ne, aka ga mariagayin a bainar jama’a, lokacin da ya halarci jana’izar wani tsohon shugaban na Faransa, Jacques Chirac.

Jawabin Emmanuel Macron bayan rasuwar Valery Giscard d'Estaing

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.