Turai

Tarayyar Turai zata yaki labaran kariya

Wasu daga cikin kungiyoyi dake yaki da labaran karya
Wasu daga cikin kungiyoyi dake yaki da labaran karya Aude WTFake

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da matakan da zata dauka wajen yaki da yada labaran kariya a Turai, a daidai wannan lokaci da labarai masu firgita mutane dangane da allurar rigakafin corona ke cigaba da yaduwa.

Talla

Kungiyar tarayyar turai zata kuma rage yawan amfani da siyasa a tallace tallace da kuma kare rayuwar ‘yan jaridu, hakan zai kasance daga cikin manufofinta na demokkradiya.

Mataimakiyar Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar Vera Jourova ta shaidawa kamfanin dillancin labaran faransa AFP cewa suna tattaunawa ne a kan hare hare masu muni, saboda haka yada labaran kariya bai dace ba.

Uwargida Vera Jourova ta kara da cewa a shirye Shugabannin Kungiyar suke, su  karfafa dokar yaki da yada labaran kariya, wadda a cikin shekarar 2018 aka gabatar.

Dokar da ta samu sa hannun manyan kamfanonin sadarwa irin su Google, facebook, Twitter, Microsoft kana a watan yunin shekarar 2020 ta sa hannun kamfanin sadarwa ta Tiktok.

Sai dai a dayan bangaren, kungiyar tarayyar turai EU ta ce aiki da matakan ta kadai ba zai magance matsalar yada labaran kariya ba sai ta hada kai da wasu hukumomi na Kasa da Kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.