Najeriya

Yan Sanda 3 sun nitse a ruwa lokacin aikin zabe

Wasu daga cikin jami'an hukumar zaben Najeriya
Wasu daga cikin jami'an hukumar zaben Najeriya REUTERS/Tife Owolabi

Rundunar yan Sandan Najeriya ta ce jami'an ta guda 3 suka mutu lokacin da suka nitse a ruwa a karamar hukumar kudancin Ijaw dake jihar Bayelsa,lokacin gudanar da zaben cike gurbi yau asabar.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya bayyana cewar yan Sandan sun gamu da hadarin ne  lokacin da kwale-kwale dake dauke da su ya kife da su a kan hanyar su ta zuwa wurin aiki.

Asimin Butswat,kakakin yan Sandan jihar Bayelsa ya tabbatar da aukuwar lamarin a kan hanyar Oporoma,cibiyar karamar hukumar,sai dai yace basu iya tattance adadin jami'an na su da suka gamu da hadarin ba.

Jihar Bayelsa na daga cikin jihohin Najeriya da ake gudanar da zabubbukan cike gurbi yau asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.