Kotun Afirka ta bukaci Benin ta sauya dokokinta
Wallafawa ranar:
Kotun Kare hakkin bil'adama ta kasashen Afrika ta bukaci hukumomin Jamhuriyar Benin da su sauya wasu daga cikin dokokin kasar da Majalisa ta amince da su da ake kallon su a matsayin wadanda suka saba wa dokokin duniya.
Kotun da ke zama a birnin Arusha na kasar Tanzania ta bukaci dawo da dokar da ta bai wa jama’a damar gudanar da zanga zanga da kuma soke duk wasu dokokin da suka saba ka’ida a cikin watanni 3.
Ana sa ran gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Benin a rånar 11 ga watan Afrilun shekarar 2021, amma 'yan adawa tare da kungiyoyin fararen hula sun koka kan shirin zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu