Najeriya-Coronavirus

Najeriya: Korona ta harbi sama da mutane 1300 a cikin kwanaki 4

Wani ma'aikacin lafiya yana daukar  samfurin gwajin cutar corona daga wani mara lafiya.
Wani ma'aikacin lafiya yana daukar samfurin gwajin cutar corona daga wani mara lafiya. AFP

A cikin kwanaki 4 a jere Najeriya ta sanar da da cewa tana samu mutane dari 300 da suka harbu da cutar Cornavirus duk rana, inda a ranar Lahadi ta ce mutane 318 sun harbu.

Talla

Adadin wadanda cutar ta harba a kasar ya kai sama da dubu 69, bayan da aka samu mutane dubu 1 da dari 315 da cutar ta kama daga ranar Alhamis zuwa Lahadi.

Adadi na 318 da aka samu a ranar Lahadi ya kai jimillar wadanda cutar ta harba zuwa dubu 69 da dari 2 da 55 a fadin kasar.

Babu wanda cutar ta kashe a ranar Lahadi, abin da ke nufin cewa adadin wadanda suka mutu yana nan a dubu 1 da dari da 80.

Cikin sama mutane dubu 69 da cutar ta harba, an salami dubu 64 da dari 7 da 74 daga asibiti bayan da aka yi musu magani, yayin da har yanzu akwai sama da dubu 3 da ke fama da kcutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.