najeriya

Najeriya za ta fara biyan 'yan tasi, bas, achaba tallafin naira dubu 30

Gwamnati Najeriya za ta ba 'yan bas da achaba tallafin naira dubu 30. (Business Highlights)
Gwamnati Najeriya za ta ba 'yan bas da achaba tallafin naira dubu 30. (Business Highlights) Business Highlights

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin bayar da tallafi ga masu aikin hannu da harkar sufuri, a ci gaba da shirinta na tabbatar da dorewar tattalin arziki, da kuma kudirinta na rage radadin annobar coronavirus ta wajen agaza wa masu kanana da matsakaicin sana’o’i.

Talla

Kaddamar da wanna shiri na tallafa wa masu harkar sufuri a farkon makon da ya gabata ya biyo bayan nasarar da aka samu a shirin da aka kaddamar na tallafa wa masu sana’o’in hannu ne a ranar 1 ga watan Oktoba.

Yayin da masu sana’o’in hannu da aka tantance suka fara samun tallafin naira dubu 30, wanda sau daya ake bayarwa, ‘yan Najeriya da ke harkar sufuri da suka hada da masu tukin bas bas, keke Napep da ‘yan achaba da masu tura baro da amalanke da sauransu suna da damar cin moriyar wannan shirin.

Ya zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba, jimillar masu sana’o’in hannu dubu 59 ne aka biya su wannan tallafi a jihohi 24 na kasar da suka hada da birnin Abuja, Lagos, Ekiti, Kaduna, Borno, Kano, Bauchi, Anambra, Abia, Rivers, Plateau, Delta, Taraba, Adamawa, Bayelsa, Edo, Ogun, Ondo, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Enugu, Ebonyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.