An cika shekara guda da kisan sojojin Nijar 71 a Inates

Wani sojin Nijar a yankin Sahel.
Wani sojin Nijar a yankin Sahel. AFP Photo/MICHELE CATTANI

A ranar Alhamis  aka cika shekara guda da kisan da 'yan ta’adda suka yi wa sojojin Jamhuriyar Nijar 71 a harin da suka kai sansanin su dake Inates, kusa da iyakar Mali.

Talla

Wannan hari da na Shinagoder ya sanya gwamnatin Nijar sauke ministan tsaro da kuma kwamandojin sojin kasar sakamakon asarar rayukan dakarun da akayi.

Daga bisani gwamnati ta kaddamar da bincike kan badakalar cinikin makamaı bayan anyi zargin cewar sojojin ba su da isassun kayan aiki duk da makudan kudaden da aka zuba domin samar musu.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da ake yaki da Boko Haram da kuma 'yan ta’adda a iyakar Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.