Afrika ta Kudu-Coronavirus

Mutane fiye da dubu 6 sun kamu da Coronavirus cikin kwana guda a Afrika ta kudu

Bayanai sun ce a wannan karon cutar ta fi kama matasan da shekarunsu ya fara daga 15 zuwa 19.
Bayanai sun ce a wannan karon cutar ta fi kama matasan da shekarunsu ya fara daga 15 zuwa 19. Michele Spatari/AFP/Getty Images

Gwamnatin Afirka ta kudu ta ce annobar korona ta sake barkewa a cikin kasar kashi na biyu, yayin da a jiya kawai aka samu mutane dubu 6 da 79 da suka harbu da cutar a cikin sa’oi 24.

Talla

Ministan lafiya Zweli Mkhize ya ce an samu karuwar cutar ne a yankuna 4 da suka hada da Western Cape da Eastern Cape da KwaZulu Natal da Guateng.

Ministan ya ce an fi samun masu kamuwa da cutar ne tsakanin matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19 wanda ya ce yana da nasaba da bukukuwan rawa da ake gudanarwa a yankin.

Mkhize ya yi gargadin cewar idan lamarin ya ci gaba da gudana haka harkokin lafiyar kasar za su tabarbare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.