Amurka ta yaba wa 'yan sandan Najeriya da suka kama wadanda suka sace Ba'Amurke

Jami'an 'yan sandan Najeriya.
Jami'an 'yan sandan Najeriya. The Guardian Nigeria

Amurka ta yaba wa ‘yan sandan Najeriya sakamakon banjitar da suka yi wajen cafke wadanda suka sace wani BaAmurke.

Talla

Tibor Nagy, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka ne ya yi wannan jinjina.

An sace Mr Phillippe Walton, wanda dan kasar Amurka ne a gonarsa dake kauyen Masalata a Jamhuriyar Nijar, a cikin watan Oktoba.

Idan ba a manta ba, gwamnatin Amurka ta aike da dakaru na musamman don aikin ceto Mr. Walton, kuma tawagar ta yi nasarar ceto shi.

Sai dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da damke wasu matasa 2 da ake zargi da hannu a wannan aika aikar, Aliyu Abdullahi, mai shekaru 21, da Aliyu Umaru, mai shekaru 23, dukkanninsu daga jihar Sokoto.

Rundunar ‘yan sandan na Najeriya ta ce matasan 2 na cikin wani gungun masu satar mutane mai mutane 15 a kasar, wanda wasu mutune biyu, Barte Dan Alhaji da Dan Buda ke jagoranta.

Mr. Nagy ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter, inda yake jinjina ga ‘yan sandan Najeriya da suka ceto Ba’amurken da aka sace a watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.