Amurka ta cire Sudan daga jerin kasashen da ke taimaka wa ta'addanci

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump (AP / JPP)

A Litinin din nan Amurka ta cire Sudan daga jeri kasashen da ta ke zargi da taimaka wa ayyukan ta’addanci, shekaru 27 bayan da  antaya sunan Sudan din a kundin sunayen kasashen da ke bai wa ‘yan ta’adda gudummawa, kamar yadda ofishin jakadancin Amurkar a Khartoum ya sanar.

Talla

A shafinsa na Facebook, ofishin jakadancin Amurka ya wallafa sakon da ke cewa, sakataren harkokin wajen kasar ya sanya hannu a takardar da ke bayyana cire Sudan daga kasashen da ke taimakon ta’addanci a duniya, kuma matsayinta na kasar da aka wanke daga wannan zargi zai fara aiki ne daga 14 ga Disamba.

A watan Oktoba, shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta cire Sudan daga jerin kasashen da ake zargi da taimaka wa ayyukan ta’addanci, matakin da sabuwar gwamnatin kasar ta kagara a dauka, duba da yadda hakan ke hana masu zuba jari daga waje shiga kasar.

A cikin kunshi yarjejeniyar, Sudan ta amince ta biyar diyyar dala miliyan 335 ga wadanda suka sha da kyar, da ma iyalan wadanda hare haren da aka kai ofisoshin jakadancin Amurka a Kenya da Tanzania a shekarar 1998 suka rutsa da su.

Gwamnatin wucin gadin Sudan, wacce ta dare madafun iko bayan kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar da ta gabata, ta kuma amince da Isra’ila a matsayin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.