Bakonmu a Yau

Majalisar dattijan Najeriya ta yi karatun na biyu kan Kudurorin kafa rundunar‘peace corps’

Sauti 03:41
Hukumar yan Sandan Najeriya
Hukumar yan Sandan Najeriya AFP

Majalisar dattijan Najeriya ta yi karatun na biyu kan Kudurorin kafa sabbin rundunonin jami’an tabbatar da zaman lafiya na ‘peace corps’ da kuma rundunar mafarauta domin taimakawa jami’an tsaro wajen kawo karshen matsalolin tsaron da suka addabi sassan kasar ta Najeriya.

Talla

Matakin na zuwa a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari gami da manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar ke cigaba da shan caccaka kan kalubalen da ya dabaibaye sha’anin tsaro a sassan kasar.

Kan haka muka tattauna da masanin tsaro a Najeriya, Aminu Bala Sokoto (Squadron Leader mai ritaya).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.