Cote d'Ivoire

Alassane Ouattara ya nada abokin hamayyarsa a matsayin Minista

Shugaban kasar Senegal Alassane Ouattara.
Shugaban kasar Senegal Alassane Ouattara. John MacDougall/Pool via REUTERS/File Photo

Shugaban Kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya nada tsohon dan takarar shugaban kasar Kouadio Konan Bertin a majalisar ministocin sa domin kula da shirin sasanta jamą’ar kasar.

Talla

Bertin wanda ya zo na 2 a zaben shugaban kasar da ya gudana ranar 31 ga watan Oktoba zai rike mukamin ministan sasanta jama’a, kamar yadda shugaban ya yi alkawarin kafawa lokacin rantsar da shi.

Kasar Cote D’Ivoire ta fada rikicin siyasa tun lokacin da shugaba Ouattara ya bayana aniyor sa ta tsayawa takarar zabe sakamakon rasuwar dan takarar Jam’iyyar sa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.