Gwamnan Borno ya gana da shugaban Chadi kan 'yan gudun hijirar Najeriya

Shugaban kasar Chadi Idris Deby yayin karbar bakuncin gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum
Shugaban kasar Chadi Idris Deby yayin karbar bakuncin gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum RFI hausa/Abba

Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum ya gana da shugaban Chadi Idris Deby lokacin da ya ziyarci kasar domin ganin halin da Yan gudun hijirar Jihar sa ke ciki da kuma shirya yadda za’a mayar da su gida.

Talla

Yayin ganawa da shugaban, Zulum ya bayyana godiya ga gwamnatin Chadi kan yadda take kula da Yan gudun hijirar da kuma bayyana aniyar cigaba da aiki tare da su wajen kwashe su domin mayar da su gida.

Kafin ganawar da shugaba Deby, Gwamna Zulum ya ziyarci sansanın Yan gudun hijirar dake Baga Sola inda ya bayyana musu aniyar sa ta mayar da su gıda, yayın da ya rabawa iyalai 5,000 dake wurin naira miliyan 50.

Su dai wadannan yan gudun hijirar sun fito ne daga karamar hukumar Kukawa.

Gwamna Zulum ya kai irin wannan ziyara kasashen Kamaru da Nijar inda ya gana da Yan gudun hijira daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.