Borno-Chadi

Gwamnan Borno ya ziyarci 'yan Najeriya dake gudun hijira a Chadi

Shugaban kasar Chadi Idris Deby yayin karbar bakuncin gwamnan jihar Borno daga Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum a birnin Ndjamena
Shugaban kasar Chadi Idris Deby yayin karbar bakuncin gwamnan jihar Borno daga Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum a birnin Ndjamena RFI hausa/Ahmed Abba

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Chadi, inda bayan isa birnin Ndjamena ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijirar daga Najeriya da adadinsu ya kai dubu 5, a garin Bagasula. 

Talla

'Yan gudun hijirar sun tsere daga Najeriya ne tun shekarar 2014, sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram kan garuruwansu dake iyaka da kasar Chadi.

Wakilinmu a kasar ta Chadi Mustapha Tijjani Mahadi ya aiko mana da rahoto kan ziyarar gwamnan na Borno.

Rahoto kan ziyarar da gwamnan Borno ya kaiwa 'yan gudun hijira a kasar Chadi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.