Jam'iyyar Lumana ta goyi bayan Mahamane Ousmane a zaben Nijar

Mahamane Ousmane tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar
Mahamane Ousmane tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar RFI

A Jamhuriyar Nijar ,jam’iyyar Lumana ta tsohon Shugaban Majalisar kasar kuma jagoran yan adawa Hama Amadou bayan wani taro da daukacin ya’an jam’iyyar ta bukaci magoya bayan ta da su zabi tsohon Shugaban kasar Mahamane Ousmane a zaben shugabancin kasar na ranar 27 ga watan disambar 2020.

Talla

A watan Nuwamba ne kotun fasalta kundin Tsarin Mulki a Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da takarar Madugun jam’iyyun adawar kasar Hama Amadou dake neman shugabancin kasar.

Da yake yanke hukuncin shugaban kotun fasalta kudin tsarin mulki Bouba Mahamane ya ce, Hama Amadou dake takara karkashin jam’iyyar adawa ta Moden Lumana bai cancanci tsayawa takara ba, saboda hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso dake kansa.

Sakamakon rashin tsayawa takarar shugabancin kasa ta madugun yan adawar Nijar Hama Amadou, Jam’iyyarsa ta Lumana ta umurci magoya bayan ta da su jefawa Mahaman Usman na RDR Canji tun zagaye na farko,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.