An kashe naira biliyan 9 wajen bada Rashawa a fannin Shari’ar Najeriya - ICPC

Wasu lauyoyi a Najeriya
Wasu lauyoyi a Najeriya REUTERS

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, tace kimanin naira biliyan 9 da miliyan 400 aka kashe a kasar wajen bada cin hanci ga masu ruwa da tsaki a fannin Shari’a don sauya hukuncin kotuna.

Talla

Sabon rahoton na ICPC yace an biya kaso mafi yawa na kudaden rashawan ne domin tasiri kan shara’o’in da suka shafi zabe da siyasa, daga shekarar 2018 zuwa 2020.

Hukumar yaki da rashawar ta ICPC ta kasafta jumillar kudaden toshiyar bakin na naira biliyan 9 da kusan rabi zuwa ajujuwan kudaden da masu ruwa da tsakin a harkar shari’a suka nemi ko dai a basu, ko aka yi musu tayi, ko kuma ma aka biyasu kuma suka dafe.

Cikin rahoton ICPC ta bayyana tuntubar ma’aikata 901 a fannin shari’ar Najeriya, 638 daga cikinsu Lauyoyi, Alkalai 124, sai kuma sauran ma’aikata da suka hada da magatakarda da akawu 25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.