Afrika

'Yan Afrika ta Kudu dubu 11 ke kamuwa da coronavirus duk rana a tsawon mako

Wata ma'aikaciyar jiyya a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu yayin baiwa wani mutun kyallen rufe fuska kafin yi masa gwajin cutar coronavirus.
Wata ma'aikaciyar jiyya a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu yayin baiwa wani mutun kyallen rufe fuska kafin yi masa gwajin cutar coronavirus. Shiraaz/Xinhua News Agency via Getty Images

Afrika ta Kudu ta zama kasa ta farko a nahiyar Afrika da adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus ya zarta miliyan 1.

Talla

Sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar sun nuna cewa a halin yanzu yawan masu cutar ta coronavirus a Afrika ta Kudu ya kai miliyan 1 da dubu 4 da 413, daga cikinsu kuma cutar ta kashe dubu 26 da 735.

A makon jiya kididdigar hukumomin lafiya ta nuna cewar, akalla mutane dubu 11 da 700 ake ganowa sun kamu da cutar kowace rana tsawon kwanaki 7 jere da juna.

Sake barkewar annobar ta coronavirus karo na 2 a Afrika ta Kudun ya sanya hukumomin kasar soma shawara kan yiwuwar sake yiwa jama’a kulle bayan dakatar da zirga-zirga, matakin da ake sa ran shugaban kasar Cyril Ramaphosa zai sanar yayin jawabin da zai yiwa ‘yan kasar a tsakiyar makon da muke shiga.

Kawo yanzu akalla mutane dubu 62 da 649 annobar coronavirus ta aika barzahu, daga cikin miliyan 2 da dubu 658 da 646 da suka kamu da cutar.

Morocco ce kasa ta 2 da annobar tafi yiwa ta’adi bayan halaka mata mutane dubu 7da 240, daga cikin dubu 432da 79 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.