Najeriya

Gwamnatin Najeriya za ta yaki matsalar hauhawan farashin abinci - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. @MBuhari

Shugaban Najeriya Mohammed Buhari ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta yaki matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci a sabuwar shekara mai kamawa.

Talla

Shugaban ya yi alkawarin ne a yayin taronsa karo na biyar da Kwamitin Tattalin Arziki na fadar shugaban kasa a birnin Abuja a jiya Talata.

Shugaban ya kuma umarci babban bankin kasar CBN da ka da ya bai wa ‘yan kasuwa kudi don shigo da abinci daga ketare, yana mai cewa, a yanzu akwai jihohi bakwai a Najeriya da ke samar da shinkafar da ta wadaci kasar, kuma dole mu ci abin da muke nomawa a cewarsa.A watan Disamba na shekarar 2019 rufe kan iyakokin ta da gwamnatin Najeriya ta yi na tsawon watanni yanzu haka, ya zama tamkar gobarar Titi, inda wasu mazauna kauyukan jihar sokoto ke ta samun arziki sakamakon aikin sarrafa shinkafa da suke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.