Bakonmu a Yau

Koma bayan ilimi a Jihar Barno dake Najeriya

Sauti 03:52
Wasu daga cikin makarantu a kasashen Afrika
Wasu daga cikin makarantu a kasashen Afrika Marka/Universal Images Group via Getty Images

Jihar Barno dake arewa maso gabashin Najeriya na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar koma bayan ilimi a kasar tun ma kafin bullar Boko Haram, dalili ke nan da kungoyoyin kasa da kasa da ma gwamnati dukufa wajen ganin an farfado da harkar sakamakon tabarbarewar tsaro da jihar ke fuskanta yanzu haka.

Talla

Bullar annobar korona da irin matakai da gwamnatoci ke dauka don hana yaduwarta na maida hannun agogo baya,kamar yadda Malam Shu’aibu Abubakar darakatan makarantar Bara’imul Imam, kuma mataimakin shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu na jihar Barno ya shaidawa Ahmad Abba yayin ziyararsa birnin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.