Duniya-Coronavirus

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince da ingancin alluran rigakafin Covid 19

Allurar rigakafin coronavirus da kamfanin Pfizer ya samar
Allurar rigakafin coronavirus da kamfanin Pfizer ya samar Reuters

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana amincewa da ingancin alluran rigakafin cutar coronavirus na hadin gwiwar kamfanonin Pfizer da BioNTech, abinda ya baiwa karin kasashe damar gaggauta odar alluran.

Talla

Maganin rigakafin na Pfizer da BioNTech dai shi ne na farko da hukumar lafiya ta duniya ta amince a yi amfani da shi kan annobar Korona. A watan Nuwamban shekarar 2020 hukumar Lafiya ta Duniya ta yaba da ingancin sabuwar allurar riga-kafin cutar coronavirus duk da cewa ta bukaci karin lokaci kafin kammala tantance tasirinsa a jikin dan Adam.

Shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya danganta kwayar cutar Covid-19 da zama mummuna da ke farma daukacin sassan jikin dan Adam, yana mai gamsuwa da ingancin sabuwar allurar riga-kafin da kashi 95 cikin 100.

Ghebreyesus ya sanar da taron manema labarai cewa kasashen da ke ci gaba da nuna sakacin yaki da cutar, na wasa ne da wuta  a hannunsu.

Kafin umarnin na WHO dai, tuni sama da kasashe 50 ne suka soma yiwa al’ummominsu alluran rigakafin cutar ta Korona, shekara guda bayan barkewarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.