An soma zaman makoki a Nijar
Wallafawa ranar:
Hukumomin kasar Janhuriyar Nijar sun sanar da fara zaman makoki tun daga jiya littini bayan mummunar harin da ‘yan bindiga suka kai jihar Tilaberi inda suka kasha mutane dari karshen mako.
Bayanai na nuna ‘yan bindigan masu ikirarin jihadi da karfin tsiya bisa babura suka shiga kauyukan biyu suka yi ta kisan bayin Allah.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Nijar ya bada tabbacin cewa an kara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ‘yan bindigan ke kai hare-hare.
Wasu rahotanni na nuni cewa maharan sun kai hari ne a matsayin fansa wadanan kauyuka,kasashe na ci gaba da yin Allah wadai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu