Uganda

Shekaru 36 na Museveni a karagar mulkin Uganda

Yuweri Museveni, shugaban Uganda.
Yuweri Museveni, shugaban Uganda. Ug.gov

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya sake tsayawa neman takarar shugaban kasar da za’a gudar ranar Alhamis mai zuwa,wanda ya d’are kujeran mulkin karon farko,a shekarar 1986, kuma tun wancan lokacin, ake damawa dashi, a matsayin shugan da yake cikin jerin shugabannin da suka jima akan kujerar shugabancin kasashen su.

Talla

A matsayin sa na shugaban ‘yan tawaye a wancan lokacin, ya taka babban rawa wajen hamb’arar da gwamnatin ‘yan kama karya, karkashin jagorancin Idi Amin, a shekarar 1979. Bai tatsaya nan ba, ya ci gaba da yakin sun kuru dan ganin ya kawo karshen mulkin Shugaba Milton Obote a shekarar 1986 kuma tun lokacin yake jagorancin kasar.

Jim kadan, da hawarsa kujerar mulkin kasar , ya aiyana cewa matsalar Afrika itace, na shugabani masu zaman dirshan wato har illa masha Allah akan kujerar mulki.

Hakan dai, shi yasa ya samu karb’uwa a wajen al’ummar kasar, amma da tafiya ta yi tafiya, sai gashi gwamnatin nasa ta gaza tabuka abun azo a gani . A halin yazu dai kasar tana daga cikin jerin kasashen da ke fama da talauci a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.