Faransa

Faransa na nazarin hanyoyin yakar Covid 19

Franministan Faransa  Jean Castex
Franministan Faransa Jean Castex TF1

Ana kyautata zaton a yau laraba taron hukumar koli dake kula da kiwon lafiya a Faransa ta sanar da sabon matakin da zata dauka wajen rage yaduwar annobar coronavirus, wace sabon nau’inta mai saurin yaduwa ya fara samun gurbin zama a Faransa.

Talla

Hukumar yaki da cututuka ta gudanar da taron ta a fadar shugaban kasar Faransa dake Paris yau laraba, a wani lokaci da ake dakon sanarwar gwamnatin Jean Castex wacce za ta gabatar da shawarwarin da aka tsaida a gobe alhamis

Shugaban gwamnatin ta Faransa a jiya talata ya sanar da cewa, a halin yanzu faransawa sun san ciwon kansu, don haka nan gaba dokar takaita lokacin fita ta wadatar, ba sai an sake killace mutane a karo na 3 a cikin gidajensu ba.

Haka kuma karin jihohi 25 da tuni suke cikin dokar takaita lokutan fita gida daga 6 na yamma zuwa 6 na safe, nan gaba zata zama ta bai daya a ko ina cikin fadin kasar, kamar yadda majiyoyi da dama na kusa da gwamnati suka sanar.

Wannan kuwa na zuwa ne lura da yadda hukumar kimiya dake baiwa gwamatin Faransa shawarwarin hanyoyin da ya kamata a bi wajen dakile yaduwar cutar ta covid 19 ke nuna matukar damuwarta dangane da yadda ake kara samun mutanen dake harbuwa da annobar a Faransa

Annobar Covid-19 a kullum sai ci gaba da zama karfen kafa take ga tsarin kiwon lafiyar faransawa, tare da yawan mutane dubu 1 660 da suka kamu a cikin kasa da sa’o’i 24 a kasar, haka kuma sama da wasu dubu 19 sabbin sakamakon da ma’aikatar kiwon lafiyar Faransa ta sanar a marecen jiya talata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.