Wasanni-Kwallon kafa

PSG-Marseille -El Classico

Magoya bayan kungiyar Paris Saint Germain a Paris
Magoya bayan kungiyar Paris Saint Germain a Paris GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP

A Faransa , zuwa an jima Paris Saint Germain za ta fafata da Marseille a gasar cin kofin zakarun Faransa.Wannan dai ne karo na 99 da kungiyoyin biyu ke haduwa,yayinda Barcelona za ta ketse reni da Real Sociedad a Spain.

Talla

Watanni hudu kenan da aka fuskanci yan matsalloli tsakanin magoya bayan kungiyoyin PSG da Marseille, a lokacin Angel di Maria ya tofa yahu zuwa dan wasa Alvaro Gonzalez.

Jaridu da dama a kasar ta Faransa suka yi tuni da wancan lokaci na ranar 13 ga watan Satumban shekarar da ta gabata, hakan ya kuma baiwa mai tsaron gidan PSG Keylor Navas da cewa samun dan wasa da aikata haka ,tamkar babban kuskure ne.

Tarihi na nuni cewa, kungiyar PSG ta lashe kofin sau 7,ana kuma sa ran sabon mai horar da kungiyar Mauricio Pochenttino da ya maye gurbin Thomas Tuchel zai dawo da son wannan kungiya ta PSG a zukatan magoya bayan ta.

Dan wasan Brazil Neymar da ya share kusan wata daya ya na jinya ,zai dawo fagen tamola a wannan fafatawa da Marseille.

PSG ta dawo da karfi a cewar Mauricio Pochenttino, inda yan wasa da suka hada da Neymar ,Presnel Kimpembe, Danilo Pereira da Leandro Paredes, dukanin su za su kasancewa a fagen karawar da PSG za ta yi Marseille a wannan gasar Classico ta Faransa.

Bangaren Marseille, komi ya kankama a cewar mai horar da kungiyar dan kasar Fotugal Villas Boas, da yanzu haka zai baiwa yan wasa kama daga Pol Lirola damar nuna ta su bajinta a wannan haduwa ta yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.