Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

'Yan tawaye sun kai hare-hare gab da birnin Bangui na Afrika ta tsakiya

Wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bangui na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
Wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bangui na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. FLORENT VERGNES / AFP

‘Yan tawayen Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya sun kaddamar da mabanbantan farmaki har guda biyu a gab da babban birnin kasar Bangui yau Laraba.

Talla

Ma’aikatar cikin gida ta bakin Minista Henri Wanzet Linguissara ta ce tuni Sojin kasar suka fattaki maharan wadanda suka kaddamar da farmakin a tazarar kilomita 12 da birnin na Bangui.

Harin shi ne irinsa na farko da ‘yan tawayen masu kalubalantar shugaba Faustin Archange Toudera suka kaddamar tun bayan zaben kasar na ranar 27 ga watan Disamba da shugaban ya lashe.

Ministan cikin gidan na Africa ta tsakiya Henri Wanzet da ke shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP yadda farmakin ya faru ya ce harin ya rutsa da wasu dakarun Soji 2 da ke bakin aiki,

Laftanar Kanal Abdoulaziz Fall kakakin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSCA da ke cikin kasar, ya ce babu ko da mutum guda da ya mutu ko ya samu rauni yayin farmakin wanda ya faru da misalin karfe 6 na safiyar yau, amma yaki da ‘yan tawayen zai ci gaba don tabbatar da zaman lafiya a Kasar.

Tun cikin watan jiya ne Rasha da Rwanda suka aike da dakarunsu kasar don daidaita al’amura bayan boren ‘yan tawayen da suka tilasta gaza gudanar da zabe a wasu sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.