Mali

Dakarun Faransa sun halaka 'yan ta'adda 15 akan iyakar Mali da Burkina

Sojojin Faransa yayin sauka daga jirginsu na yaki a Mali.
Sojojin Faransa yayin sauka daga jirginsu na yaki a Mali. @EtatMajorFR/Twitter

Rundunar sojin Faransa tace ta halaka mayakan ‘yan ta’adda 15 yankin Boulikessi dake Mali a gaf da iyakar kasar da Burkina Faso, inda mayaka masu alaka da Al’Qaeda suka matsa wajen kai hare-hare.

Talla

Dakarun Faransar sun kuma kame wasu mayakan 4, da kwace makamai masu yawa da kayayyakin hada bama-bamai.

A farkon makon nan dakarun Faransa na rundunar Barkhane suka fuskanci caccaka a ciki da wajen Mali, bayan da aka zarge su da amfani da jirgin yaki wajen halaka fararen hula 20 dake halartar bikin aure a kauyen Bounti, farmakin da Faransar ta dage kan cewar mayakan ‘yan ta’adda ta kaiwa, zalika bata halaka farar hula ba.

Lamarin dai ya auku ne a ranar 3 ga wannan wata na Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.