Uganda

Sojoji sun yiwa gidan jagoran 'yan adawar Uganda kawanya

Dan takarar neman shugabancin kasar Uganda Bobi Wine
Dan takarar neman shugabancin kasar Uganda Bobi Wine Sumy SADRUNI / AFP

Jagoran ‘yan adawa kuma dan takara a zaben shugabancin kasar Uganda Bobi Wine yace sojoji sun yiwa gidansa kawanya, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Talla

Matakin jami’an tsaron ya zo ne sa’o’i bayan da Wine yayi ikirarin lashe zaben da ya gudana a ranar Alhamis, tare da yin watsi da sakamakon kidayar kuri’un da ya nuna shugaba mai ci Yoweri Museveni ke kan gaba da tazara mai yawa.

Jagoran ‘yan adawar na Uganda ya kuma koka kan cin zarafin magoya bayansa da jami’an tsaro suka yi, ta hanyar duka da kuma korarsu daga sa ido kan gudanar zaben ranar Alhamis a wasu yankunan yammaci da arewacin kasar, zalika a wasu yankunan an baiwa masu kada kuri’a takardun zaben ‘yan majalisu ne kawai banda na shugaban kasa.

‘Yan takara 11 ne suka fafata a zaben kasar Uganda, wanda shugaba Museveni mai shekaru 76 ke neman wa’adi 6 bayan shafe shekaru 34 yana mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.