Duniya

An soma allurar korona a India da Brazil

'Yan  uwan wani mutun da annobar Korona ta halaka, yayin kokarin binne gawarsa a birnin New Delhi na kasar India
'Yan uwan wani mutun da annobar Korona ta halaka, yayin kokarin binne gawarsa a birnin New Delhi na kasar India Danish Siddiqui/Reuters

A yau asabar kasashen Duniya da suka hada Indiya ,Brazil sun soma allurar rigakafin cutar coronavirus zuwa al’uma.A Indiya akala mutane bilyan daya da dubu dari uku ne za su amfana da wannan allura yayinda rahotanni ke nuni cewa mutan kasar na dar-dar da wannan allurar.

Talla

Yayin gudanar da taron Kwamitin kar ta kwana na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bukaci hukumomin kasashe da su gaggauta bincike mai zurfi kan sabbin nau’ikan cutar coronavirus da suke yaduwa cikin gaggawa a tsakanin akalla kasashe 50, bayan soma bayyana a Birtaniya, Afrika ta Kudu da kuma Brazil.

A karshen taron masu ruwa da tsakin da ta jagoranta, kwamitin na hukumar lafiya yaki amincewa da kudurin wasu kasashe na tilastawa matafiya nuna shaidar karbar rigakafin Korona bayan ga na gwajin cutar kafin bazu izinin shige da fice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.