Tunisa

Matasan Tunisia sun ci gaba da bore bayan kame mutum 600

Tunisians protest the lack of change since the 2011 revolution.
Tunisians protest the lack of change since the 2011 revolution. Alessandro Bajec

Kwana na hudu a jere al’ummar Tunisia musamman matasa na bore, wanda ya juye zuwa arangama tsakaninsu da jami’an bayanda gwamnatin kasar ta tsananta dokar takaita walwala don dakile yaduwar Coronavirus.

Talla

Rundunar ‘yansandan Tunisia ta ce ko a jiya Litinin sai da ta kame matasan 600 wadanda suka tayar da rikici ta hanyar kona tayoyi da kuma rufe manyan hanyoyin baya ga jifan jami’an tsaro.

Tuni dai matasan ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta ke ci gaba da sabunta kiran bukatar karuwar masu gangamin don bijirewa gwamnati dai dai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki wanda annobar coronavirus ta sake assasa shi.

Boren dai ya faro ne sa'o'i kalilan gabanin zagayowar ranar juyin-juyi halin kasar da ya hambarar da gwamnatin dadadden shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali cikin watan Janarun 2011.

Matasan Tunisia na zargin gwamnatin kasar da gaza daidaita al'amura cikin shekaru 10 tun bayan juyin-juyin halin wanda ya sake jefa al'umma cikin matsin rayuwa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ruwaito yadda aka shafe tsawon dare ana arangama tsakanin jami’an tsraon da matasan masu bore musamman a Sfax birni na biyu mafi girma a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.