Najeriya: 'Yan bindiga sun sace wani hakimi a Adamawa
Wallafawa ranar:
‘Yan bindiga a jihar Adamawa dake Najeriya sun sace wani basarake, Ardo Mustapha.
Rahotanni sun ce an sace basaraken ne a ranar Litinin da misalin karfe 12 na dare a gidansa dake garin Mayo-Farang, a karamar hukumar Mayo - Belwa ta jihar.
Ardo Mustapha wanda shine hakimin gundumar Mayo Farang, kuma sarkin Noman Adamawa, an sace shi ne bayan ya dawo daga balaguron da ya yi zuwa Abuja, babban birnin Najeriya.
Wani mazaunin yankin, wanda lamarin ya firgita shi, ya ce an yi ta dauki ba dadi ta wajen musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da ‘dogarai da ‘yan bangan yankin, amma abin takaici, sai da aka yi awon gaba da basaraken.
Da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya ce rundunar ta baza ‘yan sanda don ceto basaraken, yana mai tabbatar da cewa za a kubutar da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu