Najeriya

Matsalolin Najeriya: Sake fasalin kasa kadai ba zai wadatar ba - Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. Daily Trust

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce sake fasalın kasar kawai ba zai magance dimbin matsalolin da suka dabaibaye ta ba, inda ya bukaci al’ummar kasar da su lalubo wasu hanyoyin na daban da za’ayi amfani da su wajen shawo kan su baki daya.

Talla

Jonathan ya ce ci gaba da mahawara kan wannan batu ba zai taimaka ba, domin kuwa dole sai Yan Najeriya sun sake fasalin tunanin su da kuma irin gudummawar da zasu bayar wajen gina kasa.

Tsohon shugaban ya ce irin matsalolin da ake fuskanta a matakan kasa basu yi hannun riga da wadanda ake da su a Jihohi da Kananan Hukumomi da ma cikin al’umma ba.

Daya daga cikin matsalolin da ya gabatar ita ce rashin yarda tsakanin 'yan Najeriya, wanda ya ce ya zama wajibi a kawar da wannan kafin a samu kasa mai inganci.
Jonathan ya ce babu yadda za’a sake fasalin Najeriya ba tare da shawo kan wadannan batutuwa da suka raba kań jamą’ar kasar ba, kamar na kabilanci da addini da rashin kishin kasa da nuna banbanci.

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne wajen taron da Jaridar 'Daily Trust' ta shirya domin tattauna batutuwan da suka addabi Najeriya a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.