Mutane miliyan 34 na bukatan agajin gaggawa a yankin Sahel - OCHA

Wasu 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira a Kamaru, yayin da suka yi layi don karbar tallafin abinci.
Wasu 'yan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake gudun hijira a Kamaru, yayin da suka yi layi don karbar tallafin abinci. UNHCR / C. TIJERINA

Mutane kimanin miliyon 34 da rabi ne ke bukatar agajin gaggawa a yankin Sahel, wadanda tuni kungiyoyin agaji suka tantance miliyon 22 daga cikinsu, wannan adadi na zuwa ne lokacin da aka samu kashi 46 na kudaden tallafi daga kasar Amurka ciki harda na yaki da cutar Corona inji kungiyar OCHA.

Talla

Yanayin samar da kayan agaji a yankin na Sahel ya tabarbare a 2020 sakamakon cutar corona inji Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, wace tace mutane miliyon 14 ne ke cikin matsanancin yanayi da ya kai na ha’ula’i.

Adadin mutanen miliyon 14 ya rubanya a shekara daya, wannan bai rasa nasaba da rashin tsaro a tsakiyar yankin na Sahel da ya shafi kasashe irinsu Burkina Faso da Mali da Niger da kuma Chadi, inda kungiyoyin ‘yan ta’ada ke ci gaba da addabar jama’a.

Wannan lamari dai ya haifar dubban ‘yan gudun hijira a cikin kasashensu, dama ketare, adadin da ya ninka har sau 20 tun 2018, Kutsen yan bindiga a yankin tafkin Cadi da arewaci da gabashin Najeriya da Burkina Faso na iya sa a fuskanci yunwa, kuma al’ummomi na bukatar abinci, wurin zama, ilimi, tsaro da kiwon lafiya, baya ga matsallar karamcin abinci, yankin na Sahel na fama da wasu matsalolin na canjin yanayi, talauci karuwar al’umma kamar wutar daji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.